West Brom za ta tsawaita kwantiragin Berahino

Saido Berahino Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A karon farko Ingila ta gayyato shi cikin tawagar 'yan kwallonta

Kulob din West Brom ya fara tattaunawa kan tsawaita kwantiragin Saido Berahino domin ya ci gaba da buga tamaula har zuwa 2017.

Dan wasan mai shekaru 21, ya zura kwallaye takwas a raga a kakar bana, kuma West Brom na fargabar dan wasan zai iya tafiya wata kungiyar domin kwadayin buga gasar zakarun Turai.

Shugaban kulob din Jeremy Peace ya sanar ta Intanet cewa "Mun fara tattaunawa da Berahino domin tsawaita kwantiraginsa da mu".

A karon farko tawagar kwallon kafar Ingila ta gayyato Berahino domin ya buga mata wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Turai da za su yi da Slovenia a Wembley ranar 15 ga watan Nuwamba.