2015: Morocco ba za ta karbi bakuncin AFCON ba

CAF Logo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption CAF tana tsaka mai wuya wajen nemo kasar da za ta maye gurbin Morocco

Hukumar kwallon kafar Afirka, CAF ta tabbatar cewa Morocco ba za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka kamar yadda aka tsara tun farko ba.

Sai dai kuma CAF ba ta sanar da kasar da za ta maye gurbin Moroco ba, domin gudanar da gasar da ya kamata a fara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu.

Kwamitin amintattun CAF ya kuma amince da korar Morocco daga wasannin, wacce ya kamata ta samu tikiti a matsayin mai masaukin baki.

Mahukuntan Morocco na bukatar a dage gasar zuwa shekarar badi, sakamakon tsoron kamuwa da cutar Ebola.