Real Sociedad ta dauko David Moyes

David Moyes Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin zai fara wasan farko da Deportivo cikin Nuwamba

Kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad ta Spaniya ta dauko David Moyes a matsayin sabon koci da zai jagorance ta.

Moyes, mai shekaru 51, ya maye gurbin Jagoba Arrasate, bayan da Sociedad ta sallame shi sakamakon kasa tabuka rawar gani a kakar bana, inda kungiyar ke mataki na 15 a kasan teburin La Liga.

Wannan ne karon farko da kocin zai horar da wata kungiya tun lokacin da Manchester United ta sallame shi a watan Afirilu, bayan kwashe watanni 10 tare da su.

Moyes dan kasar Scotland ya rattaba kwantiragin da za ta kare a watan Yuni 2016, kuma zai fara jagorantar kungiyar a karawar da za yi da Deportivo ranar 22 ga watan Nuwamba.