Didier Zokora ya ki amsa kiran Ivory Coast

Didier Zokora
Image caption Zokora ya ce ya yi ritaya ne bayan da ya tuntubi hukumar kwallon kafar kasar

Dan kwallon Ivory Coast, Didier Zokora ya ki amsa kiran da kasar ta yi masa na ya buga mata wasannin neman tikitin shiga gasar kofin nahiyar Afirka, sakamakon ritayar da ya yi.

Kocin kasar ne Herve Renard ya gayyato dan wasan mai shekaru 33, domin ya buga karawar da za su yi da Saliyo da Kamaru.

Zokora, wanda ya yi ritaya daga buga wa kasarsa wasa a watan Satumba ya ce "Ta dole ce ta sa na daina buga wa kasata wasa domin lokacin hakan ya yi, kuma ya kamata a bar wa 'yan baya".

Dan wasan -- wanda yanzu yake taka leda a Turkiya -- shi ne dan wasan da ya fi yawan buga wa Ivory Coast wasanni, saboda ya buga mata karawa har sau 121.

Ivory Coast za ta kara da Saliyo a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka ranar 14 ga watan Nuwamba sannan ta fafata da Kamaru kwanaki biyar bayar bayan hakan.