'Rooney daya ne daga cikin fitattun 'yan wasa'

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rooney ne kyaftin din Ingila a inda ya gaji Steven Gerrard

Tsohon kyaftin din Ingila Gary Lineka ya ce Wayne Rooney ya cancanci a martaba shi a daya daga cikin 'yan kwallon kasar da suka fi kwazo.

Rooney, mai shekaru 29, zai buga wa Ingila wasa na 100 a karawar da za ta yi da Slovenia ranar Asabar, kuma shi ne dan wasa na hudu a jerin 'yan wasa da suka fi zura kwallaye a raga, inda ya zura 43.

Lineka tsohon dan kwallon Ingila wanda ya ci wa kasar kwallaye 48 ya ce "Ya kamata a martaba Rooney cikin kololuwar 'yan wasan da suka fi fice a kasar".

Rooney ya fara buga wa Ingila wasa a karawar da ta yi da Australia a watan Fabrairun 2003 a matsayin dan wasa mai karancin shekaru da ya fara buga mata tamaula a lokacin yana da shekaru 17 da haihuwa.

Sai dai Theo Walcott ya karya wannan tarihin, amma dai Rooney ne dan kwallon Ingila mai karancin shekaru da ya fara buga mata wasa.