AFCON 2015: Za a bayyana kasar da za ta karbi bakunci

Issa Hayatou Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hayatou ya ce ranar da aka tsayar na fara gasar na nan daram

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, za ta fitar da sunan kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Nahiyar Afirka nan da kwanaki biyu ko uku masu zuwa.

Shugaban hukumar kwallon kafar Afurka Issa Hayatou ne ya bayyana hakan a wata kafar yada labarai a lokacin da aka tattauna da shi ranar Talata.

Shugaban ya kuma jaddada cewar lokacin da aka tsayar na fara gasar daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu na nan babu canji.

Tun a ranar Talata CAF ta sanar da cewar Morocco ba za ta karbi bakuncin gasar kofin nahiyar Afirka na badi ba, sakamakon tsoron kamuwa da cutar Ebola.

An yi ta rade-radin cewa kasar Angola ce za ta maye gurbin Morocco, wadda ta taba daukar bakuncin gasar kwallon kafar Afirka mafi girma a nahiyara a shekarar 2010.

Sai dai kuma wani mamba na kwamitin amintattun hukumar kwallon kafar Angola Joao Lusevikueno ya shedawa BBC cewar kasarsa bata da niyyar karbar bakuncin gasar a badi.