Ronaldo zai kai karar masu zarginsa da zagin Messi

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan biyu suna kan ganiyarsu a harkar kwallon kafa

Cristiano Ronaldo ya karyata ikirarin da ake masa cewa yana kiran Lionel Messi da inkiyar sunan batsa.

A sabon littafin da aka wallafa a kan Messi dan kwallon Barcelona, an bayyana dan wasan Real Madrid yana yawan ambaton dan wasan Argentina da munanan kalamai.

Tun a baya an yi ta rade radin rashin jituwa tsakanin Ronaldo dan kwallon Portugal mai shekaru 29 da Messi dan wasan Barcelona mai shekaru 27.

Ronaldo ya rubuta a shafinsa na sada zumunta a Facebook ce wa "wannan zargin ba gaskiya bane, kuma na umarci lauya na ya shigar da wadanda ke da hannu a wannan zargin kara a kotu".

'Yan wasan biyu sun kafa tarihi da dama a kwallon kafa, ciki har da yin kankankan da Raul a 'yan wasan da suka fi zura kwallaye a gasar zakarun Turai, a inda kowannensu ya zura kwallaye 71 a raga.

Saura kwallaye biyu Messi ya karya tarihin dan wasan da ya fi yawan zura kwallo a gasar La Liga, inda ya ci kwallaye 250 a wasanni 285.

A kakar La Ligar bana, Ronaldo ne kan gaba wajen yawan zura kwallaye a raga, inda ya zura 18, Messi kuwa kwallaye 7 ya zura a raga a bana.