Chelsea ta ci ribar sama da fam miliyan 18

Chelsea Fc Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea har yanzu babu kulob din da ya doke su a bana a Premier

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bada sanarwar cewa ta samu ribar sama da fam miliyan 18 a watanni shidan farkon shekarar nan, duk da cewar bata dauki kofi a bara ba.

Chelsea wacce take a birnin Landan, wannan ne karo na biyu da ta samu riba cikin shekaru 10, tun lokacin da attajiri dan kasar Rasha Roman Abramovich ya sayi kungiyar.

Kungiyar tace sabuwar yarjejeniya da ta kulla da gidajen talabijin da kuma sayar da 'yan wasa da ta yi da suka hada da Juan Mata na daga cikin musabbabin samun ribar da ta yi.

A kakar wasanni ta bana Chelsea tana matsayi na daya a gasar Premier kuma har yanzu ba a doke ta ba a wasa, kuma ita ce ta daya a rukunin da suke na gasar cin kofin zakarun Turai.

A shekara ta 2012, Chelsea ta bayyana samun ribar sama da fam miliyan daya a karon farko karkashin Abramovich, sannan ta sanar da faduwa a shekarar 2013.