Rahoton FIFA a kwai kura-kurai — Garcia

Micheal Garcia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Garcia ya ce an sauya wasu batutuwan da ya binciko kan zargin

Rahoton da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar kan zargin cin hanci da rashawa a karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2018 da 2022 da ta wanke kanta yana dauke da kura-kurai.

Lauyan da ya binciki zargin na tsahon shekaru biyu, Michael Garcia ya ce a cikin rahotansa an canja wasu batutuwa da shaidu da shawarwari da ya bayar.

Rahoton da aka wallaha a shafuka 42, ya wanke Rasha da Qatar da soso da sabulu kan zargin cin hancin karbar bakuncin gasar kofin duniya na 2018 da 2022.

Haka kuma rahotan ya zargi hukumar kwallon Birtaniya kan kokarin kaucewa ka'ida da bata martabar FIFA.

Bayanan da Garcia ya yi awanni bayan rahoton da FIFA ta fitar, ya kara tada shakkun hanyoyin da FIFA ta bada karbar bakuncin kofin duniya ga Rasha da Qatar a shekarar 2010.