Nigeria ta dauki matakan rage rikicin NFF

NFF Logo
Image caption NFF ta sha fama da rikice-rikece tun bayan kammala gasar kofin duniya

'Yan majalisar dattijjai a Nigeria sun zartar da wani kuduri da zai yi gyara a kan yadda ake gudanar da hukumar kwallon kafar kasar NFF, domin kaucewa yawan takun saka da FIFA.

Sanatocin na fatan sauya dokar da ta bada ikon yadda za a gudanar da mulki a hukumar kwallon kafa ta NFF, da ikon kwamitin amintattun hukumar.

Kudirin ya amince da zaman NFF a matsayin mai cin gashin kanta, kamar yadda FIFA ta tanada, da kuma hana kai hukumar kara wata kotu da ba ta FIFA ba.

Nigeria ta sha fama da saka kafar wando daya da FIFA karo da dama, tun lokacin da aka kammala gasar cin kofin duniya a Brazil.

Hukumar kwallon kafar Nigeria NFF ta dogara ne da samun kudin shigarta ta wajen gwamnati, da ya kai dala miliyan daya da raba, kuma kaso 90 cikin dari daga jihohi ake samun kudaden.