FIFA ta wanke Qatar daga zargin rashawa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alkalin ya kuma wanke Rasha, wadda za ta karbi bakuncin gasar a shekara ta 2018

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya ta wanke kasar Qatar daga zargin cin hanci da rashawa.

Hukunci ya share fagen gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar ta Qatar a shekara ta 2022.

Alkalin kwamitin da ke kula da da a na hukumar FIFA ne ya yanke hukuncin bayan an gudanar da wani bincike.

Inda ya ce babu wata shaida da za a iya kafa hujja da ita ta sake yin nazari a kan wanda zai karbi bakuncin gasar.