AFCON: Equatorial Guinea ta maye gurbin Morocco

Hakkin mallakar hoto CAF
Image caption Morocco ta janye saboda Ebola

An bayyana Equatorial Guinea a matsayin kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin Afrika da za a buga a shekara ta 2015.

Equatorial Guinea ta maye gurbin Morocco wacce ta janye daga batun daukar bakuncin gasar saboda cutar Ebola da ta barke a wasu kasashen yammacin Afrika.

Sanarwar da hukumar CAF ta fitar, ta ce a kasar za a buga gasar daga ranar 17 ga watan Junairu zuwa 8 ga watan Fabrairun 2015.

A shekara ta 2012, Equatorial Guinea tare da hadin gwiwar Gabon suka daukin bakuncin gasar cin kofin Afrika.