AFCON 2015: Kasashe 9 sun sami tikiti

Afcon 2015 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption kasashe tara ne suka sami tikitin buga gasar badi

Kasar Afirka ta kudu tana daga cikin kasashe shida da suka sami tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na badi a wasannin da aka fafata ranar Asabar.

Sauran kasashen da suka sami tikiti a ranar Asabar din sun hada da Kamaru, da Zambia da Burkina Faso da Gabon da kuma Senegal.

Tun a farko Algeria da Cape Verde da Tunisia ne suka fara samun tikitin buga gasar cin kofin Afirkan na badi da Equatorial Guinea da za a fara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu.

Sai a ranar Laraba ne za a buga wasannin karshe na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da zai tabbatar da sauran kasashen da za su sami izinin shiga gasar.

Ga wasannin da za a fafata ranar Laraba:

Congo DR, vs Sierra Leone Ivory Coast vs Cameroon Mali vs Algeria Ethiopia vs Malawi Guinea vs Uganda Niger vs Mozambique Zambia vs Cape Verde Ghana vs Togo Nigeria vs South Africa Sudan vs Congo Burkina Faso vs Angola Gabon vs Lesotho Senegal vs Botswana Tunisia vs Egypt