ATP World Tour: Federer da Djokovic wasan karshe

federer djokovic
Image caption Wannan ne karo na 37 da Federer da Djokovic za su fafata

Roger Federer zai kara da Novak Djokovic a wasan karshe na cin kofin zakarun kwallon Tennis na duniya wato ATP World Tour Finals da ake fafatawa a Landan ranar Lahadi.

Federer wanda yake a matsayi na biyu a jerin 'yan wasan da suka fi yin fice a wasan a duniya, ya kai karawar karshe ne, bayan da ya doke Stan Wawrinka da ci 4-6 7-5 7-6 (8-6).

Shi kuwa Novak Djokovic wanda shi ne ke rike da kofin kuma na daya a iya kwallon tennis a duniya ya casa Kei Nishikori ne da ci 6-1 3-6 6-0.

Federer da Djokocic sun fafata a wasanni karo 36, Federer ya samu nasara a wasanni 19, Djokovic ya lashe karawa 17, da haduwa sau 12 a manyan wasanni.