Girka ta raba gari da kocinta Ranieri

Claudio Ranieri Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ranieri tsohon kocin Chelsea ya karbi aikin horar da Girka a watan Yuli

Hukumar kwallon kafa ta kasar Girka ta sallami kocin tawagarta Claudio Ranieri, har ma ta maye gurbinsa da Kostas Tsanas a matsayin rikon kwarya.

Girka wacce ta dauki Ranieri a watan Yuli, ta kuma sallame shi ne bayan da tsibirin Faroe ta lallasa 'yan wasan kasar da ci daya mai ban haushi a gida a ranar Juma a.

Tsohon kocin Chelsea, Ranieri, mai shekaru 63, ya jagoranci kasar a wasanni uku da aka doke su da buga canjaras daya a wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai.

Nasarar da tsibirin Faroe ta samu ita ce ta farko a babbar karawa tun daga shekarar 2011, kuma ta 20 tun daga shekarar 1988.