AFCON 2017: Kasashe hudu na zawarcin gasar

Afcon Logo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe hudu ne ke zawarcin karbar bakuncin gasar kofin Afirka na 2017

Kasar Masar na daya daga cikin kasashe hudu dake zawarcin karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2017.

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta ce sauran kasashen dake son karbar bakuncin wasannin sun hada da Algeria da Gabon da kuma Ghana.

Tuni kuma CAF ta ki amincewa da zawarcin da kasar Kenya da Sudan da kuma Zimbabbwe suke yi, saboda sun kasa cika sharuddan karbar bakuncin wasannin.

CAF na neman kasar da za ta maye gurbin Libya, wacce ta janye daga karbar bakuncin gasar sakamakon rikicin da ake yi a kasar.

Kasar Equitorial Guinea ce za ta karbi bakuncin gasar 2015, wacce ta maye gurbin Morocco, kuma za a fara wasannin ne daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu.