An ci tarar Sunderland fam 20,000

Sunderland Everton Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland ta raba maki da Everton a karawar gasar Premier

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar Sunderland fam 20,000, saboda tsaiko da ta kawo a karawar da suka buga da Everton.

Wasan na gasar Premier sun tashi kunnen doki ranar 9 ga watan Nuwamba, bayan da 'yan wasan Sunderland suka kasa kwantar da hankalinsu lokacin da aka bai wa Everton fenariti.

Dan wasan Everton Seamus Coleman aka yi wa keta a da'ira ta 18, kuma nan take 'yan wasan Everton suka zagaye alkalin wasa Lee Mason kan korafin fenaritin.

Leighton Baines ne ya buga ya kuma zura kwallon a raga da ya bai wa Everton maki guda a fafatawar.