UEFA: Za ta hukunta Croatia kan yamutsi

Italy Croatia Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Kocin ya ce za a hukunta su amma baya tuninin hukuncin zai yi tsauri

Kocin tawagar kwallon Croatia, Niko Kovac ya ce yana sa ran hukumar kwallon kafar Turai Uefa, za ta hukunta su dangane da yamutsin da ya faru a karawar da suka yi a Italiya.

Italiya ce ta karbi bakuncin Croatia a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai, inda suka tashi kunnen doki, sai dai kuma magoya bayan Croatia sun kawo tsaiko a lokacin wasan.

Sau biyu alkalin wasa Bjorn Kuipers yana dakatar da wasa, sakamakon jefa abubuwa masu tartsatsi cikin fili da suka dunga turnike fili karo da dama.

Kocin ya ce hakika UEFA za ta hukunta su, amma baya tunanin hukumar za ta rage musu maki daga cikin hukuncin da za ta yanke.

Croatia ce ke matsayi na daya a rukuni na tara, inda ta lashe wasanni uku da buga canjaras daya a wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin ta nahiyar Turai.