'Yan kwallo za su hada kai don yakar Ebola

Fight Ebola Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sama da mutane 5,160 cutar Ebola ta hanlaka

Manyan 'yan kwallon kafar duniya sun hada kansu tare da hukumar lafiya ta duniya, domin kara fadakar da al'umma don kauce wa kamuwa da kwayar cutar Ebola.

Cikin manyan 'yan wasan sun hada da Cristiano Ronaldo, da Neymar, da Didier Drogba, da kuma Philipp Lahm.

A kamfen din da suka yi wa lakabi "'yan wasa 11 za su yaki Ebola", zai kunshi wayar da kai, da bullo da hanyoyin kaurace wa kamuwa da cutar Ebola.

'Yan wasan za su dinga aika saukakan sakwanni 11 da suka shafi kula da lafiya, tare da hadin gwiwar hukumomin lafiya na duniya da suke yakar Ebola.

Kowanne sako zai kunshi hoton 'yan wasa da za a tsara ta fina finai da radiyo da manyan allunan talla, da kuma a jikin kyallaye.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce kimanin sama da mutane 5, 160 ne suka mutu sakamakon cutar Ebola, galibinsu a kasashen Guinea, da Liberia, da kuma Saliyo.