A kauracewa gasar kofin duniya — Bernstein

World Cup
Image caption Ana zargin FIFA kan cin hanci da rashawa kan bakuncin gasar kofin duniya

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Ingila David Bernstein, ya yi kira ga kasashen Turai da su kauracewa gasar cin kofin duniya na 2018, har sai FIFA ta yi gyara.

Bernstein ya ce yanzu lokaci ya yi da ya kamata a dauki hanyoyin da suka kamata don gyara tsarukan hukumar kwallon kafar duniya.

Ya kara da cewa Ingila kadai ba za ta iya kawo wannan gagarumin sauyin ba, dole sai an hada karfi da karfe shi ne za a iya kawo sauyin.

Haka kuma ya bukaci shugaban FIFA Sepp Blatter ya sauka daga kan kujerar shugabancin hukumar, sai dai ya ce hakan zai yi wuya a kawar da shugaban daga kan kujerar.

Bernstein ya ce gasar kofin duniya babu kasashen Turai za ta zama lami, kuma hakan ne zai sa FIFA ta yarda ta aiwatar da gyararrakin da muke fatan hukumar ta yi.