Kofin Duniya: FIFA ta shigar da korafi

FIFA Logo Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A shekarar 2010 FIFA ta bai wa Rasha da Qatar izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na 2018 da 2022

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta shigar da korafi ga atoni janar na Switzerland da ya shafi karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na 2018 da 2022.

Korafin ya shafi dai-dai kun mutanen da ke da hannu kan hanyoyin da ake bi wajen karbar bakuncin wasannin.

Shugaban FIFA Sepp Blatter ya wanke Rasha da Qatar kan zargin cin hanchi da Rashawa kan karbar bakuncin kofin duniya, tare da shawarar da alkali Hans-Joachim Eckhert ya ba shi a rahoton da ya wallafa mai shafuka 42.

Alkali Eckhert ya ce ba a samu wasu kwararan shaidu da za a iya tuhumar wadan da ake zargi a lokacin da suka yi zawarcin karbar bakuncin wasannin ba.