Luka Modrich zai yi jinyar watanni uku

Luka Modric Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luka Modric yana kan ganiyarsa a kulob din Madrid a bana

Dan kwallon Real Madrid Luka Modric zai yi jinyar watanni shida, bayan da ya ji rauni a wasan da ya buga wa Croatia.

Dan wasan mai shekaru 29 ya ji raunin ne a karawar da suka yi da Italia a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.

Real Madrid ta sanar da cewa Modrich ya ji rauni a cinyarsa, amma ba ta sanar da tsawon lokacin da zai yi jinya ba.

Sai dai kuma hukumar kwallon kafar Croatia ta ce dan wasan zai dawo taka leda ne a cikin watan Janaitun badi.

Modric yana cikin 'yan kwallon da suke buga wa Madrid wasanni akai - akai, kuma tuni kulob din ya samu kai wa wasan gaba na cin kofin zakarun Turai.