Philipp Lahm ya karya kafa

Philipp Lahm Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayern Munich ta yi bakinciki da Lahm zai yi jinya har watanni uku

Kyaftin din Bayern Munich Philipp Lahm, zai yi jinyar watanni uku, bayan da ya karya kafa a lokacin da yake atisaye da kulob dinsa ranar Talata.

Kulob din ya ce abin takaici ne da za suyi rashin Lahm, wanda ya yi ritaya daga buga wa kasarsa Jamus tamaula a watan Yuli, bayan kammala gasar cin kofin duniya.

Bayern Munich wacce babu kungiyar da ta doke ta a gasar bana, za ta fafata da Hoffenheim ranar Asabar a gasar cin kofin Bundesliga.

Sannan kuma zata ziyarci Manchester City a gasar cin kofin Zakarun Turai mako mai zuwa.