Ingila ta doke Scotland da ci 3-1

Scotland England Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ingila ta doke Scotland da ci 3-1 a filin Celtic Park

Tawagar Ingila ta doke Scotland da ci 3-1 har gida a wasan sada zumunta da suka buga a filin wasa na Celtic Park ranar Talata.

Oxlade-Chamberlain ne ya fara zura kwallon farko saura minti 13 a tafi hutun rabin lokaci, daga baya Rooney ya kara ta biyu minti biyu da dawo wa daga hutu da kuma ta uku a minti na 85.

Scotland ta zare kwallo daya ne ta hannun dan wasanta Robertson a saura minti na bakwai a tashi daga wasa.

Sauran sakamakon wasannin sada zumunta da aka buga:

R. of Ireland 4 - 1 USA Japan 2 - 1 Australia Slovakia 2 - 1 Finland Belarus 3 - 2 Mexico Greece 0 - 2 Serbia Slovenia 0 - 1 Colombia Austria 1 - 2 Brazil Romania 2 - 0 Denmark Hungary 1 - 2 Russia Argentina 0 - 1 Portugal Italy 1 - 0 Albania