Nigeria ba za ta gasar cin kofin Afirka ba

Mikel Obi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ba za ta sami damar kare kambunta a badi ba

Nigeria mai rike da kofin nahiyar Afirka na kwallon kafa ta kasa samin tikitin shiga gasar cin kofin na badi domin kare kambun ta, bayan da suka tashi wasa 2-2 da Afirka ta Kudu.

Afirka ta kudu ta zura kwallayenta biyu ne ta hannun Tokelo Rantie, ita kuma Nigeria ta farke kwallayenta ta hannun Aluko.

Tashi wasa 2-2 da suka yi, ya sa Nigeria ta koma mataki na uku da maki takwas, wanda Congo ta doke Sudan a Khartoum da ci 2-0.

Tuni Afirka ta Kudu ta sami tikitin shiga gasar cin kofin Afirka da za a fara ranar 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu a Equitorial Guinea.

Ga jerin kasashen da suka sami tikitin shiga gasar:

Algeria, Burkina Faso, Cameroon, Cape Verde, Congo, Gabon, Ghana, Guinea, Ivory Coast, Mali, Senegal, South Africa, Tunisia, Zambia, da kuma Mai masaukin baki Equatorial Guinea.