Ingila za ta kara da Faransa da Jamus

England Qualifier Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila na fatan taka rawa a gasar cin kofin nahiyar Turai

Tawagar kwallon kafar Ingila za ta kara da Faransa da kuma Jamus a wasan sada zumunta domin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Turai da za a fara a shekarar 2016.

Haka kuma hukumar kwallon kafar Ingilar na tattaunawa da kasar Netherlands da Spaniya domin fafatawa da su a wasannin sada zumuntar.

Wasannin za su taimakawa Ingila fuskantar kalubalen da za ta tunkara a gasar cin kofin nahiyar Turai, wadda take matsayi na daya a rukuni na biyar na neman tikitin shiga gasar.

Kazalika Ingilar na fatan karawa da Italiya ranar 31 ga watan Maris da kuma Jamhuriyar Ireland a Dubin ranar 7 ga watan Yuni.

Ingila ta doke Sloveniya da ci 3-1 a Wembley a makon jiya, ta kuma lashe dukkan wasanni hutu na neman tikitin shiga gasar cin nahiyar Turai da ta buga.