Kwallon kafar Italiya na yin baya - Conte

Italian Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Italiya na fatan taka rawa a gasar cin kofin nahiyar Turai idan ta sami tikiti

Kocin tawagar kwallon kafar Italiya Antonio Conte ya ce kwazon kwallon kafar Italiya yana yin baya, saboda karancin 'yan wasa matasa masu kwarewa.

Italiya ta doke Albania da ci daya mai ban haushi ranar Talata, kuma a gasar kofin duniya da aka kammala a Brazil ba ta haura wasannin cikin rukuni ba,

Conte, ya ce 'yan wasa matasa da suke samun tikitin buga wa tawagar wasanni basu da cikakkiyar kwarewa.

Italiya tana matsayi na biyu a rukunin da suke buga wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da maki 10 daga cikin wasanni hudu da ta buga.