Ivory Coast za ta fuskanci hukuncin CAF

Ivory Coast fitch Invation
Image caption Magoya bayan Ivory Coast sun fada cikin fili domin murnar samun tikitin gasar Afirka

Kila hukumar kwallon kafar Afirka ta hukunta Ivory Coast, sakamakon shiga fili da magoya bayanta suka yi, bayan da suka sami tikitin shiga cin kofin Afirka na badi.

Yamutsin ya faru ne bayan da Ivory Coast ta tashi wasa kunnen doki da Kamaru ranar Laraba, da hakan yasa ta kare a matsayi na biyu a rukuni na hudu.

CAF ta ce tana jiran ta karbi rahoton alkalin wasa da abubuwan da zai rubuta a rahotansa kafin ta san abin da ya kamata ta yi.

Ana sa ran CAF za ta tattauna kan abin da ya faru a Ivory Coast da sauran batutuwa da suka shafi wasan kwallon kafa a taronta da za ta gudanar ranar 1 ga watan Disamba.