Buffon ya tsawaita kwantiraginsa da Juventus

Gianluigi Buffon Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Buffon ya buga wa Juventus wasanni 400 a karawa daban - daban

Mai tsaron ragar Juventus Gianluigi Buffon ya sake tsawaita kwantiraginsa da kulob din na tsawon shekaru uku.

Buffon mai shekaru 36, ya fara buga gasar Seria A da kulob din Parma a shekara ta 1995, sannan ya koma Juventus a shekarar 2001, inda ya buga mata wasanni 400.

Mai tsaron ragar, ya lashe kofunan Serie A guda uku da Juventus da kuma karin guda biyu da aka karbe daga kungiyar bisa samunta da laifin cinikin wasanni.

Buffon ya kuma lashe kofin duniya da Italiya a shekarar 2006, kuma har yanzu shi ne yake mata tsaron raga, ya kuma buga wa kasar wasanni 146.