NFF ta dauki alhakin kasa zuwa gasar Afirka

Ahmed Uche Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ta kare a matsayi na uku ne da maki takwasa a rukuni

Hukumar kwallon kafar Nigeria NFF, ta dauki alhakin rasa samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na badi da Super Eagles ta kasa yi.

Super Eagles ta kare ne a mataki na uku a rukunin farko ranar Laraba, bayan da suka buga 2-2 da Afirka ta Kudu a fafatawar da suka yi a Uyo, Nigeria.

Shugaban NFF, Amaju Pinnicks ya ce ya kamata a bar dorawa wasu laifi a fuskanci kalubalen da ke gaban wasan kwallon kafar kasar.

Nigeria, mai rike da kofin nahiyar Afirka, ta kasa samun tikitin ne bayan da Congo ta doke Sudan da ci daya mai ban haushi.