Giroud zai buga wasa da Manchester United

Olivier Giroud Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun farko an yi hasashen sai a shekarar mai zuwa zai dawo buga kwallo

Dan kwallon Arsenal Olivier Giroud zai buga karawar da za su yi da Manchester United a gasar Premier ranar Asabar.

Tun farko an yi hasashen cewa dan kwallon Faransa, mai shekaru 28, sai a shekara mai zuwa zai fara taka leda, sakamakon karya kafa da yi a wasan da suka buga da Everton a watan Agusta.

Giroud ya shiga karawa da Everton daf a tashi wasa, inda ya zura kwallo a Goodison Park, daga baya kuma ya karya kafarsa.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya kuma ba da tabbacin cewa Mikel Artete, wanda ya ji rauni a wasan cin kofin zakarun Turai da suka kara da Anderlecht shima yana daf da warkewa.

Samun saukin da Giroud da kuma Theo Walcott suka yi zai taimakawa Arsenal dinke barakar ta.