Crystal Palace ta doke Liverpool 3-1

Crystal Palace Liverpool
Image caption Kulob din Liverpool ya koma mataki na 12 a teburin Premier bana

Kulob din Liverpool ya kara gamuwa da cikas bayan da Crystal Palace ya doke su da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na 12 da suka kara a Selhurst Park ranar Lahadi.

Liverpool ce ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Rickie Lambert a minti na biyu da fara take leda.

Crystal Palace ta farke kwallonta ta hannun Dwight Gayle, lokacin da Yannick Bolasie ya buga kwallo ta bugi turke.

Joe Ledley ne ya ciwa Palace kwallo ta biyu a dai-dai minti na 78, kuma Jedinak ya kara ta uku a bugun tazara daga yadi 25, saura minti tara a tashi daga wasa.

Liverpool ta koma matsayi na 12 a teburin Premier da maki 14, yayin da Crystal Palace ta koma mataki na 15 da maki 12.