'Ya kamata Keshi ya bar Super Eagles'

Stephen Keshi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Keshi ya kasa samun tikitin shiga gasar kofin Afirka domin kare kambu

An bai wa Stephen Keshi shawara da ya bar kocin Super Eagles salin alim tun da ya kasa kai tawagar zuwa gasar kofin nahiyar Afirka domin kare kambunta a badi.

Keshi a dai-dai wannan lokacin ba shi da kwantiragi tare da hukumar kwallon kafar Nigeria NFF.

Wani babban jami'in hukumar NFF ne ya shaida wa BBC cewa "Ya kamata Keshi ya bar Super Eagles asirinsa a rufe, ya je wani wurin ya gwada sa'arsa zai fi masa alheri".

Keshi ya shiga tsaka mai wuya a lokacin da suke buga wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka, inda NFF ta sallame shi daga aiki, ya kuma sake dawo wa karo na biyu lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya tsoma baki.

Super Eagles ta kasa samun tikitin shiga gasar kwallon kafar Afirka mafi girma da Equitorial Guine za ta karbi bakunci a badi, lokacin da suka tashi 2-2 da Afirka ta Kudu a makon jiya.