'Ba dan Sanchez ba, Arsenal sai buzunta'

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alexis Sanchez yana taka muhimmiyar rawa a kulob din Arsenal

Tsohon dan kwallon Arsenal Ian Wright, ya ce ba dan Alexis Sanchez yana taka muhimmiyar rawa ba da yanzu Arsenal tana tsakiyar teburin Premier a bana.

Kuma duk da kwazon da Sanchez din ke yi, Wright ya ce baya hangen Arsenal za ta kammala gasar Premier bana cikin 'yan hudun farko a saman teburi.

Arsenal tana mataki na takwas a teburin Premier, kuma da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester United wadda take matsayi na hudu, kuma ita ce ta doke ta 2-1 ranar Asabar.

Arsenal ta dauko Sanchez kan kudi fam miliyan 35 daga kulob din Barcelona, kuma tun daga lokacin ya zura kwallaye 12 a wasanni 19 da ya buga a bana.

Kulob din da ke Arewacin Londan ya yi rashin nasara a wasanni uku daga cikin wasanni bakwai da ya buga a baya, ya lashe wasanni biyu da yin Canjaras a karawa biyu.