Za a yi wa Thomas Vermaelen tiyata

Thomas Vermaelen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu bai buga wa Barcelona tamaula ba

Mai tsaron bayan kulob din Barcelona Thomas Vermaelen, za ayi masa aiki a kafarsa, kuma har yanzu bai fara buga wa Barca wasa ba.

Barcelona ta sayo dan kwallon, mai shekaru 29, daga kulob din Arsenal kan kudi fam miliyan 15 a watan Agusta.

Tun daga lokacin dan wasan yake jinyar raunin da ya ji a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil, lokacin da suka doke Rasha da ci daya mai ban haushi.

Daraktan wasanni na Barca Andoni Zubizarreta ya ce sun damu matuka da raunin dan wasan, kuma likitoci na duba irin jinyar da tafi dacewa da ta kamace shi.