Marco Reus zai yi jinya

Marco Reus Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan kwallon yana fama da jin rauni a wasanninsa

Dan kwallon Borussia Dortmund Marco Reus, zai yi jinya har zuwa watan Janairu, bayan dan ya ji rauni a karawar da suka tashi kunnen doki da Paderborn ranar Asabar.

Dan wasan, mai shekaru 25, bai buga wa Jamus gasar cin kofin duniya ba sakamakon raunin da ya ji, kuma bai buga wa Dortmund wasanni bakwai a kakar wasan bana ba.

Shugaban kulob din Dortmund, Hans-Joachim Watzke, ya ce dan wasan ya yi rashin sa'a, domin haka fatansa kada raunin ya kawo wa dan kwallon koma baya.

Borussia Dortmund wadda ta kare kakar bara a matsayi na biyu, yanzu tana mataki na ukun karshe, inda ta lashe wasanni uku daga cikin wasanni 12 data buga.