Copa America 2015: An raba jaddawali

Copa America 2015
Image caption Za a fara fafatawa ne a gasar 11 ga watan Yunin badi

Brazil za ta kara da Colombia a gasar Copa America na badi, bayan da aka hada kasashen a jaddawalin fara wasannin a cikin rukuni na uku.

Sauran yan rukuni na uku sun hada da Peru da Venezuela, yayin da Argentina da mai rike da kofin Uruaguay da Jamaica suke rukuni na biyu.

Kasashe 12 ne za su barje gumi a gasar cin kofin kudancin Amurka da za a fara karawa ranar 11 ga watan Yunin badi a Santiago.

Brazil ta kai wasan daf da na karshe a gasar cin kofin duniya da ta karbi bakunci, bayan da ta doke Colombia da ci 2-1.

Ga yadda aka raba rukunan kasashen:

Group A Chile, Mexico, Equador, Bolivia

Group B Argentina, Uruguay, Paraguay, Jamaica

Group C Brazil, Colombia, Peru, Venezuela