Berahino zai amsa tambayoyi bisa shan barasa

Saido Berahino Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan West Brom kuma mai buga wa Ingila tamaula

Dan wasan kulob din West Bromwich Albion kuma dan wasan gaba na Ingila, Saido Berahino zai amsa tambayoyi bayan an kama shi da laifin tuki bayan ya sha barasa.

An kama dan kwallon ne a wani titi da misalin karfe 4 na yamma a ranar 22 ga watan Oktoba.

Kwanaki biyu kafin nan ne dai Berahino ya ci wa kulob dinsa kwallaye biyu a kunnen dokin da suka yi da Manchester United.

Wata mai magana da yawun 'yan sanda ta ce dan wasan mai shekaru 21 na zuba gudu a babban hanyar da aka kama shi.

Berahino zai koma caji ofis a farkon watan Disamba mai zuwa.