Sergio dan wasa ne na musamman – Kompany

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sergio Aguero ya zura kwallaye uku shi kadai cikin mintuna biyar

Kyaftin din Manchester City Vincent Kompany ya ce Sergio Aguero dan wasa ne na musamman bayan Aguero ya zura kwallaye uku shi kadai a wasan da suka buge Bayern Munich 3-2

Kwallayen da Aguero ya zura dai sun karfafa gwiwae City a gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Kompany ya ce: "shi (Aguero) dan wasa ne da ke yin abubuwan da a zatonka ba za su yiwu ba."

Shi ma kocin kungiyar, Manuel Pellegrini ya ce dan wasan dan kasar Argentina yana "daya daga cikin 'yan wasan da suka fi iya taka leda a duniya".

A farkon wasan -- wanda suka yi a filin wasa na Etihad -- Munich na da ci 2 yayin da City ke da kwallo daya, amma Aguero ya zura kwallaye biyu mintuna biyar kafin a tashi wasan, su kuma Bayern suka kara kwallo daya.

Karin bayani