An fitar da sunayen gwarzayen masu tsaron baya

Komfany  Zabaleta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fitar da gwarzayen 'yan wasan FIFA 11 ranar 12 ga watan Janairu

'Yan wasan Manchester City Vincent Kompany da Pablo Zabaleta suna cikin masu tsaron baya su 20 da za a zabi 'yan kwallon FIFA su 11 na bana.

Sauran 'yan wasan da suke cikin takara da suke buga gasar Premier sun hada da 'yan kwallon Chelsea Filipe Luis da kuma Branislav Ivanovic.

'Yan kwallon Jamus da suka lashe kofin duniya Jerome Boateng, da Mats Hummels da Philipp Lahm da kuma 'yan wasan Real Madrid biyar na daga cikin 'yan takara.

Za a zabo masu tsaron baya su hudu da mai tsaron raga guda, da 'yan wasa uku masu buga tsakiya, da kuma masu zura kwallo a raga uku da za su zamo 'yan wasan FIFA na bana.

'Yan wasa 20,000 ne dake buga tamaula a fadin duniya za su zabo fitattun gwarzayen 'yan kwallon bana da za a bayyana ranar 12 ga watan Janairu.

Ga cikakkun ;yan wasan da za a zabo:

David Alaba (Bayern Munich); Jordi Alba (Barcelona); Dani Alves (Barcelona); Jerome Boateng (Bayern Munich); Daniel Carvajal (Real Madrid); David Luiz (Paris St-Germain); Filipe Luis (Chelsea); Diego Godin (Atletico Madrid); Mats Hummels (Borussia Dortmund); Branislav Ivanovic (Chelsea); Vincent Kompany (Manchester City); Philipp Lahm (Bayern Munich); Marcelo (Real Madrid); Javier Mascherano (Barcelona); Pepe (Real Madrid); Gerard Pique (Barcelona); Sergio Ramos (Real Madrid); Thiago Silva (Paris St-Germain); Raphael Varane (Real Madrid); Pablo Zabaleta (Manchester City)