Hukumar FA ta tuhumi Everton da West Ham

Everton  West Ham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nan da 1 ga watan Disamba hukumar FA za ta hukunta kungiyoyin biyu

Hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi Everton da West Ham kan yadda suka kasa tsawatarwa 'yan wasansu a karawar da suka yi a gasar Premier.

'Yan wasan kungiyoyin biyu sun yi ta ture junansu a wasan da Everton ta lashe West Ham da ci 2-1 ranar Asabar 22 ga watan Nuwamba.

Tun farko sai da aka bai wa dan wasan Everton McCarthy da dan kwallon West Ham Winston Reid katin gargadi tun kafin a tafi hutu.

An bai wa kungiyoyin biyu damar kare kansu daga nan zuwa 1 ga watan Disamba, kafin hukumar ta hukunta su.

Nasarar da Everton ta samu yasa ta koma mataki na tara a teburin Premier, yayin da West Ham ta sha kashi a karon farko daga cikin wasanni shidda da ta buga.