Lokaci na kara kure wa Rodgers - Grobbelaar

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rodgers yana neman yadda zai dawo da karsashin kulon din

Tsohon dan kwallon Liverpool Bruce Grobbelaar ya ce saura makwanni uku ya rage wa kocin kungiyar Brendan Rodgers a kulob din.

Liverpool, wadda take matsayi na 12 a teburin Premier bana, ta yi rashin nasara a dukkan wasannin da ta yi cikin watan Nuwamba.

Grobbelaar ya ce nan da makwanni uku idan har kocin bai dawo da tagomashin kulob din ba, masu kungiyar za su iya daukar matakin da ya da ce a kansa.

Rabon da Liverpool ta lashe wasa tun lokacin da ta doke Swansea City a League Cup ranar 28 ga watan Oktoba.