Ghana ta dauki sabon koci Grant

Avram Grant Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Avram Grant zai horas da Ghana har zuwa Fabrairun 2017

Ghana ta dauki tsohon kocin Chelsea, Avram Grant, a matsayin wanda zai horas da tawagar kwallon kafar kasar.

Grant, Mai Shekaru 59, ya karbi aiki a hannun Maxwell Konadu wanda ya horas da kasar a matsayin rikon kwarya, kuma ya rattaba hannu a yarjejeniyar watanni 27.

Grant zai fara aikin horas da tawagar kwallon kafar Ghana ranar Litinin, kuma kwantiraginsa za ta kare ne a karshen Fabrairun shekarar 2017.

Kocin, dan kasar Isra'ila yana da sati uku da ya rage masa domin shirya 'yan wasan da ya kamata su wakilci Ghana a gasar cin kofin nahiyar Afirka na badi a Equitorial Guinea.