An kwantar da Pele a asibiti

Pele Brazil Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kaishi Asibiti domin ba shi kulawar gaggawa

Tsohon dan kwallon Brazil Pele an kai shi asibiti domin ba shi kulawar gaggawa, sakamakon cutar mafitsara.

Asibitin Albert Einstein Hospital dake Sao Paulo ya ce ya dauki wannan matakin ne ganin yadda Pelen ya shiga yanayi na damuwa.

Tun farko an kai tsohon dan wasan Brazil asibiti ne ranar Litinin domin duba lafiyarsa.

Pele, wanda ya lashe kofin duniya a shekarar 1958, da 1962 da kuma 1970 ya taba zuwa asbiti ranar 13 ga watan Nuwamba, bayan da aka cire masa tsakuwa a koda.