Real Madrid ta kaddamar da sabon bajo

Image caption Real Madrid ita ce ta daya a teburin Laliga

Kulob din kwallon kafa na Spaniya, Real Madrid ya kaddamar da wani sabon bajo a wani bangare na yarjejeniyar da ya cimma da bankin Abu Dhabi.

Sauyin da aka samu a bajon shi ne na cire wata alamar gicciye da ke saman bajon.

An yi amanna cewa an cire alamar ce saboda a dadada wa Musulmi.

Sai dai za a ci gaba da amfani da ainihin bajon mai alamar gicciyen a nahiyar Turai.