Gasar 2015: "Dama na yi zaton.." Hayatou

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Issa Hayatou ya ce za su yi iya bakin kokarinsu don samar da abubuwan da ake bukata

Shugaban hukumar kwallon kafa a Afrika, Issa Hayatou ya ce dama ya yi hasashen za a samu matsala a karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika ta shekarar ta 2015.

'Yan makonni kadan ne suka rage wa kasar Equatorial Guinea ta kammala shirye shirye bayan ta maye gurbin Morocco na karbar bakuncin gasar wadda za a yi daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabwairu.

Hayatou ya shaidawa BBC cewa: ''Idan nace ba za a ci karo da matsaloli ba, to ba gaskiya na ke fadi ba''.

"Ya ce a cikin watanni biyu, ba za mu iya hada komai da komai da a ke bukata ba, batare da an samu 'yan matsaloli ba''.

Hayatou ya ce akwai damuwa a game da ''tanadin samarda abinci, da matsugunnai, da sufuri, da kuma kafafen yada labarai''. Ya ce ''za mu yi iya bakin kokarinmu don samar da abubuwan da ake bukata''.