Wenger bai damu da sukar magoya baya ba

Arsenal Fans Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana matsayi na 6 a teburin Premier, bayan wasanni 13

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai damu ba da sukar da magoya bayan Arsenal ke yi masa na kasa tabuka rawar gani a kakar wasannin bana.

Gunners ta kawo karshen kamfar kofi na shekaru tara da ta yi, inda ta lashe kofin kalubale a watan Mayu, sai dai rabonta da kofin Premier tun a shekarar 2004.

Arsenal ta doke West Brom da ci 1-0 a gasar Premier da suka kara ranar Asabar, kuma tana matsayi na shidda a teburin Premier.

Sai dai a karawar magoya bayan Arsenal sun yi ta daga kyalle mai dauke da sakon mun gode da gudunmawar da Wenger ya bayar, ya kamata ya yi ritaya.

Wenger shi ne kocin da yafi dadewa a matsayin mai horar da kwallo a Premier, inda ya fara kocin Arsenal a shekarar 1996, ya kuma tsawaita kwantiraginsa zuwa shekaru uku a watan Mayu.