Zargin cin hanci kan bakuncin kofin duniya

FIFA Logo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A shekarar 2010 ne FIFA ta bai wa Rasha da Qatar izinin karbar bakuncin kofin duniya na 2018 da 2022

An kara yin sabbin zarge-zargen cin hanci a kan yadda aka zabi kasashen da zasu karbi bakun cin gasar kofin Duniya ta 2018 da 2022 wato Rasha da Qatar.

Zarge-zargen na kunshe ne a cikin wani kundin bayanan sirri da tawagar ta gabatar da bukatar Ingila ta karbar bakuncin gasar 2018 ta ce ta samu.

Jaridar Sunday Times ta Ingila ce ta wallafa wasu daga cikin zarge-zargen.

Sai dai dukkan mutanen da kasashen sun musanta zarge-zargen.

Kuma wani kwamitin bincike da hukumar FIFA din ta kafa ya wanke dukkan wadan da ake zarga.