Man City ta doke Southampton 3-0 har gida

Southampton Manchester City Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wannan karon faro da aka doke Southampton a gida

Manchester City ta koma matsayi na biyu a teburin Premier, bayan da ta doke Southampton da ci 3-0 a gasar Premier da suka buga ranar Lahadi.

Yaya Touré ne ya zura kwallon farko a minti na 51 da fara tamaula, kafin Lampard ya kara ta biyu a minti na 80, kuma Clichy ya kara ta uku saura minti biyu a tashi wasa.

Sergio Aguero wanda ya buga wa City wasa na 100 da ya buga wa kulob din bai zura kwallo a raga ba, haka kuma an bai wa Eliaquim Mangala jan kati a karawar.

Southampton wacce City ta doke ta koma mataki na uku a teburin Premier da maki 26, yayin da Manchester City ta dare matsayi na biyu da maki 27.