Gerrard ya karyata rashin jituwa da Rodgers

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana matsayi na 11 da maki 17 a teburin Premier

Kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ya karyata cewar ya samu rashin jituwa da koci Brendan Rodgers, bayan da ba a fara wasa da shi ba a karawa da Stoke City a gasar Premier.

Gerrard, mai shekaru 33, wannan ne karon farko da ba a fara wasa da shi ba a Liverpool tun daga farkon shekarar nan bayan da ya yi jinya.

Rodgers bai sa Gerrard a karawar da suka doke Stoke City da ci 1-0 a filin Anfield ba, kuma a karawar ne ya ke cika shekaru 16 da ya fara yi wa Liverpool wasa.

Sai dai kocin ya ce bai ma san a ranar ne kyaftin din ya ke cika shekaru 16 da fara buga wa kulob tamaula ba, inda ya buga wasanni 18 a bana.

Gerrard wanda ya yi ritayar buga wa Ingila tamaula bayan gasar cin kofin duniya da aka kamma a Brazil, ya buga wa Liverpool wasanni 483 ya kuma zura kwallaye 113.